Rukunin farko na alhazan Ummara guda goma daga Jamhuriyar Nijar zai tashi zuwa Saudi Arebiya a ranar Talata, 23 ga Febrairu.
Rukunin shine na farko tun bayan da Saudiya ta rufe Ummara a bara sakamakon annobar COVID-19, wato korona.
DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan Nijeriya 23 da suka tafi aikin Ummara sun sauka a Madina
Shugaban Kamfanin Sufurin Jirgin sama na Rhouda Travel and Tours, Umar Abdulhadi Alfuti ya ce kamfanin nasa ne ya samarwa alhazan su goma biza.
Ana sa ran alhazan za su tashi ne ta Ethiopian Airline ET2403 daga Filin Sauka da Tashin Jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Diori Hamani da ke Niamey, Jamhuriyar Nijar.