Hukumar Alhazai ta Jihar Yobe, ta shirya gudanar da taron bita na yini guda domin wayar da kan masu ruwa da tsaki a kan Adashin Gata na Hajji da kuma sha’anin kula da harkokin maniyyata a jihar.
Katin gayyata da hukumar ta raba ta hannun shugabanta, Alhaji Bukar Kime, ya nuna taron an shirya shi ne musamman domin wayar da kan masu ruwa da tsaki a sha’anin maniyyatan jihar game da Adashin Gata na Hajji, wanda aka fi sani da Hajj Savings Scheme wanda Hukumar Hajji ta Ƙasa(NAHCON) ta ƙirƙiro.
Taron wanda aka shirya gudanarwa tare da haɗin gwiwar Bankin Ja’iz, zai gudana ne a ranar Laraba, 3 ga watan Maris, 2021 da misalin ƙarfe 11 na safe, a babban zauren taro na Cibiyar Raya Al’adu da ke Damaturu.
Gwamnan jihar, Mai Mala Buni, ake sa ran ya zama babban baƙo a wajen taron, yayin da Sarkin Fika, Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idriss kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe, shi zai zama shugaban taro.
Ana kyautata zaton cewa taron zai taimaka wajen wayar da kan waɗanda lamarin ya shafa wajen kara musu sanin makamar aiki.