Mutumin da ya fara shiga cikin rijiyar zamzam, Yahya Koshak ya rasu

0
1

Injiniya Dakta Yahya Koshak ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a ranar Talata a Saudi Arebiya.ala

Shine mutumin da ya fara shiga cikin rijiyar zamzam domin wani gagarumin aikin yashe ta a zamanin mulkin Sarki Khalid a 1979.

Aikin yasar na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gyaran rijiyar a tarihi, inda hakan ya ƙara haɓaka ɓulɓular ruwan zamzam ɗin bayan da aka cire wasu abubuwa da suke hana gudanar ruwan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here