HAJJ 2021: Za a samu isashshiyar allurar rigakafin korona ga dukkanin alhazan Nijeriya

0
323

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Bar. Zikrullah Kunle Hassan ya tabbatar da cewa dukkanin maniyyatan Hajjin 2021 za su samu allurar rigakafin COVID-19, wacce aka fi sani da korona in dai har hukumomin Saudi Arebiya za su yadda a yi aikin Hajji a bana.

Hassan ya bada tabbacin ne a ranar Juma’a bayan da aka yi masa tambaya a yayin ganawa da manema labarai a wani ɓangare na bikin cikar shekara ɗaya da fara shugabancin hukumar.

“Muna ta tattaunawa da kwamitin kar ta kwana a kan cutar corona na fadar shugaban ƙasa (PTF). Muna aiki kafaɗa da kafaɗa. Kwamitin ya shaida mana cewa da zarar Hajjin bana ya tabbata za a yi, to za a bamu alluran rigakafin,” ya ce.

Shugaban na NAHCON ya cire fargabar da ake yi na cewa ko za a samu isashshiyar allurar rigakafin ga alhazan Nijeriya.

Ya ce Nijeriya ta kammala shirye-shirye na karɓar allurar guda miliyan 16 nan ba da daɗewa ba, ya ƙara da cewa “gaba ɗaya ma alhazan na Nijeriya ba za su wuce 100,000 ba.

Alhaji Hassan ya kuma bayyana cewa hukumar NAHCON ba za ta tilastawa kowanne maniyyaci ya yi allurar ba.

Amma kuma ya bayyana cewa idan hukumomin ƙasar Saudiyya su ka sanya yin allurar rigakafin COVID-19 ta zamto wani sharaɗi na zuwa aikin Hajjin bana, to NAHCON bata da yadda za ta yi sai dai ta yi biyayya.

Ya kuma bayyana cewa indai Saudiya ta gindaya sharaɗin, to duk wani maniyyaci da ya ƙi yadda a yi masa allurar to sai dai ya fasa zuwa Hajjin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here