Ba lallai mu tsawaita dokokin Korona ba- Saudi Arebiya

0
1

Daga Bashir Isa

Bayanai daga Ƙasar Saudiyya sun nuna ƙasar ta yanke shawarar ba za ta tsawaita wasu dokokin yaƙi da cutar korona da ta gindaya a ranar 3 da kuma 14 ga Fabrairun da ya gabata ba sakamakon samun raguwar masu harbuwa da cutar a ‘yan kwanakin nan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ne ya bada wannan labari a Juma’ar da ta gabata, yana mai danganta majiyarsa da ma’aikatar harkokin cikin gida na ƙasar.

Wannan ƙudiri na Saudiyya wanda ake sa ran ya soma aiki 7 ga Maris, zai bada zarafin ci gaba da gudanar da harkoki a gidajen cin abinci, buɗe gidajen sinima da wuraren nishaɗi da wuraren motsa jiki da dai sauransu.

Sai dai harkoki irin taron ɗaurin aure da na ma’aikatu a manyan zauren taro da otel-otel da makamantansu, dokar hanin na ci gaba da aiki har sai abin da hali ya yi.

Majiyar ta nuna buƙatar da ke akwai jama’a su yi biyayya ga dokokin yaƙi da korona da aka shimfiɗa domin ci gaba da kare lafiyar al’umma da kuma tsare nasarorin da aka samu wajen yaƙi da annobar a ƙasar kawo yanzu.

Tare da jaddada cewa za a ƙara matse ƙaimi wajen sanya ido na ganin jama’a na kiyaye dokokin yaƙi da annobar yadda ya kamata da kuma hukunta duk wanda aka samu ya take wata doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here