Yayin da ƴan Nijeriya suka dawo yin Ummara, wani rukunin na alhazan Ummara su 18 zai tashi zuwa Saudi Arebiya a ranar Juma’a mai zuwa.
Alhazan za su tafi ne ta kamfanin tafiye-tafiyen jirgin sama na Firdausi Transport Services da yake a Jihar Kano.
HAJJ 2021: Za a samu isashshiyar allurar rigakafin korona ga dukkanin alhazan Nijeriya
Alhazan za su tashi ne a jirgin Ethiopia ta Filin Sauka da Tashin Jirgin Sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja a ranar Juma’a inda a ranar a ke sa ran za su sauka a filin jirgin sama na King Abdulaziz dake Jeddah.
Shugaban kamfanin na Firdausi Transport Services, Alhaji Aliyu Abdullahi Jega,ya shaidawa Hajj Reporters cewa an yi kyakkyawan tsari na tashin alhazan.