NAHCON ta hori malamai da su rika faɗakarwa a kan jita-jita

0
362

Hukumar Hajji ta Nijeriya (NAHCON) ta gudanar da wani taron tattaunawa tare da malaman Islama na Nijeriya kan muhimmancin yakar matsalar gurbata bayanai da kuma yada jita-jita game da ingancin allurar rigakafin cutar korona.

Da yake jawabi yayin taron wanda ya gudana a ranar Litinin, 8 ga Maris, 2021 a Chelsea Hotel, Abuja, Shugaban NAHCON Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya ce an shirya taron ne don tattaunawa da malaman game da ayyukan kwamitin dattawa na hudu na hukumar da kuma neman shawarwari daga gare su a matsayinsu na tsoffin hannu kan harkokin Hajji.

Sai kuma dalilin neman su ci gaba da taimakawa da addu’o’i da kuma neman hadin kansu wajen wayar da kan al’umma game da shirin ‘Adashin Gata’ don tanadin zuwa Hajji wanda kan bai wa maniyyaci damar ajiya kada-kadan har dai a cim ma manufa.

Hassan ya shaida wa taron cewa, duk da dai har yanzu fata ake yi kan yiwuwar Hajjin 2021, amma cewa NAHCON na tuntubar Kwamitin Shugaban Kasa Kan Yaki da Cutar Korona (PTF) don tabbatar da samun zarafin kimtsa wa aikin Hajji daidai da sabbin tsare-tsaren da aka tsara a sakamako annobar korona.

Duka wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a wajen taron, sun jaddada muhimmancin wayar da kan al’umma kan cutar korona da kuma sauran ayyukan da ke da alaka da Hajji.

Taron ya bada shwarar cewa duba da aikin Hajji abu ne da ke kunshe da abubuwa da dama, akwai bukatar a wayar da kan malamai game da dokokin yaki da cutar korona domin ba su damar isar da su ga jama’a a ciki hudubobinsu.

HAJJ 2021: Za a samu isashshiyar allurar rigakafin korona ga dukkanin alhazan Nijeriya
Mahalarta taron sun yaba da irin nasarorin da NAHCON ta samu a baya-bayan, tare da bada tabbacin a shirye suke su bada hadin kan da ake bukata daga gare su.

Bayanin da ya fito ta hannun Shugabar Sashen Hulda da Jama’a na Hukumar, Fatima Sanda Usara, sun nuna taron ya samu mahalarta daga sassan kasa kuma daga cibiyoyin Musulunci daban-daban.

Manyan jami’an NAHCON, irin su Sheikh Suleiman Momoh da Alhaji Nura Hassan Yakassai da Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa da sauransu, na daga cikin wadanda suka halarci taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here