Gwamnatin Saudiyya ta ce ta amince da yi wa Ƙasar Malaysia ƙarin gurbi 10,000 daga gurbin da ya kamata ta samu na aikin hajjin bana.
Firan Ministan Malaysia, Tan Sri Muhyiddin Yassin ya ce, shi ne ya buƙaci a yi wa ƙasarsa wannan ƙarin a lokacin da ya yi wata ganawa da Yarima Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al-Saud kuma Mataimakin Ministan Tsaro, a fadar Al-Yamamah a ranar Laraba.
Yayin ziyarar kwanaki huɗu da ya yi Muhyiddin ya shaida wa manema labarai cewa, “Idan komai ya koma daidai game da aikin Hajji bayan wucewar annobar korona, za mu samu ƙarin gurbi ga maniyyatanmu.”
Ya ci gaba da cewa, Yarima ya bada amsa mai gamsarwa tare da bada tabbacin amsa buƙatar da ya nema kasancewar Saudiyya tana maraba da maniyyatan Malaysia a kowane lokaci saboda ɗa’ar da suke da ita.
Ya ce a halin da ake ciki, ayyukan faɗaɗa Makka da Madina na kan gudana domin bada zarafin iya karɓar ƙarin alhazai nan gaba.
A cewar kafar Tabung Haji, Gwamnatin Saudiyya ta shirya bada gurbin Hajji kaso 0.1 ga kowace ƙasa wanda a halin yanzu Malaysia ke da gurbi 31,600.
Ministan ya ce akwai buƙatar al’ummar Malaysia su yi haƙuri bisa taƙaitawar alhazai da aka samu a bara sakamakon annobar korona.
Ya ce akwai albishir da damar ga ‘yan Malaysia sakamakon tattaunar da ƙasashen biyu suka yi wanda hakan zai taimaka wajen sauƙaƙe sha’anin Umura da Hajji ga ‘yan Malaysia, tun daga shirye-shiryen tafiya zuwa kammala ayyukan Umura da Hajji.