An ƙaddamar da Adashin Gata na Hajji a Jihar Nassarawa

0
4

An ƙaddamar da shirin Adashin Gata na Hajji a Jihar Nassarawa, shirin da zai taimakawa maniyyata su riƙa tara kuɗaɗe domin zuwa Hajji cikin sauƙi.

Adashin Gatar, tsari ne da NAHCON tare da Bankin Ja’iz suka samar domin bai wa maniyyata damar ajiyar guzirin tafiya hajji kaɗan-kaɗan don cim ma buri.

Taron ƙaddamarwar ya gudana ne a fadar gwamnatin jihar, ranar Laraba,10 ga watan Maris a garin Lafia, babban birnin jihar, in ji wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar.

Tawagar da ta ɗauki nauyin wayar da kan jama’a game da tsarin, ta ƙunshi manyan jami’an gwamnatin jihar da na Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da na Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta Jihar (SPWB) da jami’an Bankin Jai’z da sarakuna da malamai da dai sauransu.

Gwamnan jihar Nasarawa, Engr. Abdullahi A. Sule, shi ne ya kasance mai masauƙin baƙi kuma shugaban ƙaddamar da shirin.

Baya ga gwamnan, jiga-jigan da suka halarci taron ƙaddamarwar sun haɗa da; Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Dr. Emmanuel Agbadu Akabe; Muƙaddashin Alƙalin-alƙalan Jihar, Hon. Justice Aisha Bashir Aliyu; Sakataren Gwamnatin Jihar, Barr. Muhammad Ubandoma Aliyu, Mai Martaba Sarkin Keffi, Dr Shehu Cindo Yamusa wanda ya wakilci Mai Martaba Sarkin Lafia kuma shugaban majalisar sarakunan jihar, Hon Justice Sidi Bage1.

Sauran su ne; tawagar hukumar NAHCON ƙarƙashin jagorancin Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, da tawagar Bankin Ja’iz ƙarƙashin jagorancin Muƙaddashin Manajin Darakta, Alhaji Abdulfatah Amaoo, da Suhagaban Kwamitin Mahajjata na Majalisar Dokokin Jihar, Hon. Abubakar Hassan Nalaraba da dai sauransu.

Yayin da yake jawabi, Gwamna Sule ya bayyana gamsuwarsa game da shirin, yana mai cewa shiri ne da zai taimaka wa hukumar kula da harkokin hajji don rage dogaro ga gwamnati.

Ya ƙara da cewa, tsarin zai tallafa wajen tattala arzikin maniyyata da ma na gwamnati musamman ma idan aka yi la’akari da yadda ita gwamnatin ke ƙoƙarin yin baya-baya da harkokin addini.

A nasa ɓangaren, Shugaban NAHCON Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya zayyo irin alfanun da ke tattare da shirin wanda maniyyatan za su mora.

Tare da cewa, shirin zai cim ma nasara ne kaɗai idan aka haɗa kai aka bada gudunmawar da ta dace, musamman faɗakar da jama’a don shiga shirin.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban riƙo na Bankin Ja’iz ya ce, burin shirin ne agaza wa hukumar hajji a matakin ƙasa da jiha.

Shi ma wakilin Sarkin Lafia Hon Sidi Bage 1, wato Sarkin Keffi, da sauran waɗanda suka yi magana a wajen taron, sun ce a shirye suke su bai wa Adashin Gatar cikakken goyon bayansu don kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here