NAƊIN SABON MINISTAN HAJJI/UMURA

0
432

Sarki Salman kuma Hadimin masallacin Makka da Madina, ya naɗa Dr. Essam bin Saad bin Saeed a matsayin sabon Ministan Harkokin Hajji da Umura.

Rahotanni daga Ƙasar Saudiyya sun tabbatar da cewa naɗin sabon ministan ya soma aiki ne nan take.

Dr Essam ya gaji Dr Saleh bin Tahir Benten ne inda zai ɗora daga inda ya tsaya wajen ci gaba da kula da harkokin Hajji da Umura a Saudiyya.

Minista mai barin gado Dr Saleh bin Tahir Benten, ya nuna godiyarsa ga Sarki Salman da Yarima Muhammad dangane da damar da suka ba shi wajen yi wa baƙin Allah hidima.

Benten ya bayyana haka ne ta shafinsa na twita jim kaɗan bayan da Sarki Salman ya bada umarnin maye gurbinsa da Dr Essam.

Ya ce, “Ina godiya ga mai kula da masallatai biyu masu alfarma Sarki Salman bin Abdulaziz, da Mai Martaba Yarima Muhammad bin Salman, bisa damar da suka ba ni don yi wa ƙasarmu da baƙin Mai Rahma hidima wanda hakan wani karamci ne ga rayuwata.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here