Wani rukunin Alhazan Ummara daga Nijeriya ya isa Saudiyya

0
208

Rahotanni daga ƙasar Saudiyya sun tabbatar da cewa wani rukunin Alhazan Umura daga Nijeriya sun isa babban filin jirgin sama na Sarki Abdul a Jeddah inda tuni suka kama hanyar birnin Madina domin aikin Umura.

Mahajjatan su 21, kamfanin sufuri na Firdausi Transport Services da ke Kano shi ne ya yi ɗawainiyar tafiyarsu zuwa ƙasa mai tsarki inda suka tashi ta babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe a daren da ya gabata ta jirgin Ethiopian Airline.

Shugaban kamfanin Firdausi transport services, Aliyu Abdullahi Jega, ya shaida wa HAJJ REPORTERS cewa an yi nasarar tantance duka mahajjatan a filin jirgin sama kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Madina.

Kawo yanzu, maniyyata daga Nijeriya na ci gaba da yin tururuwa zuwa ƙasa mai tsarki domin aikin Umura cikin sauƙi idan aka kwatantan da lokutan gabanin Hajjin 2020 inda Saudiyya ta dakatar da yin Umura ga waɗanda ke wajen ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here