Mataimakin Ministan Hajji da Ummara, Abdulfattah bin Sulaiman Mashat ya bayyana wani gangariyan tsari gurin kawo canji mai nagarta ga hidimar da ma’aikatan sa kai ke yiwa alhazai.
Wani rukunin Alhazan Ummara daga Nijeriya ya isa Saudiyya
Dr Abdulfattah ya bayyana cewa za a samar da tushe mai ƙwari ga jama’a da kuma ƙirƙiro da wasu sabbin tsare-tsare ga ma’aikatan sa kan inda hakan zai bada gudunmawa mai kyau wajen hidimatawa alhazai.