An gudanar da bita a kan shirin Adashin Gata na Hajji a Keffi, Jihar Nassarawa.

0
287

Hajj Reporters ta tuna cewa a bara ne dai Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta ƙaddamar da sabon shirin na Adashin Gata na Hajji, wanda a turance a ke masa laƙabi da Hajj Savings Scheme, HSS.

Ita kuwa wannan bitar Hukumar Kula da Jin daɗin Alhazai ta Jihar Nassarawa ce ta gudanar domin ƙarawa juna sani don cin amfanin shirin.

Jihar ta Nasarawa ta gudanar da bitar ne a shiyyar Keffi, wanda ya haɗa kan maniyyata daga yankunan ƙananan hukumomin Keffi, Nasarawa, Toto, Karu da kuma Kokona haɗa da yankunan rayawa na shiyyar.

Da yake buɗe taron bitar wanda ya gudana a Keffi, Sakataren Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai na Jihar Nasarawa, Malam Idris Ahmad Almakura, ya ce an shirya taron ne domin faɗakar da Musulmi da kuma maniyyata daga shiyyar game da sabon shirin Adashin Gata na tanadin tafiya Hajji da aka ƙaddamar makon jiya a Lafia, babban birnin jihar.

Malam Almakura ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen nusar da maniyyata dangane da ƙalubalan da aikin Hajjin wannan zamani ke tattare da su.

Daga nan, Idirs ya yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa irin goyon bayan da yake bai wa hukumar wanda a cewarsa hakan ya taimaka wa hukumar matuƙa wajen samun lambobin yabo a gida da ƙetare.

Malam Idris Almakura ya jaddada irin ƙoƙarin da gwamnatin Abdullahi Sule ke yi don kyautata jin ɗaɗin da walwalar maniyyata a jihar.

Daga nan ya yi kira ga maniyyatan jihar da su nuna halin ɗa’a da bada cikakkanen haɗin kansu yayin da hukumar ta himmantu da shirye-shirye.

Kazalika, Idris ya roƙi maniyyata da su yarda a yi musu allurar rigakafin korona wanda a cewarsa hakan wajibi ne a kan maniyyata, tare da cewa allurar ba ta da wata illa.

A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi wanda sakatarensa ya wakilce shi a wajen taron, ya bai wa hukumar tabbacin cewa hukumar Keffi a shirye take ta bada goyon bayanta don cim ma nasara.

Waɗanda suka gabatar da muƙala a wajen taron, Dr. Umar Yanda da kuma Dr. Ahmad Imam, baki ɗaya sun nuna buƙatar da ke akwai Musulmi su rungumi wannan shiri na Adashin Gata don tanadin tafiya Hajji.

Taron ya kammala cikin nasara tare da raba wa mahalarta takardun shaida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here