Independent Hajj Reporters, cibiyar da ke kawo rahotanni kan Hajji da Ummara a Nijeriya da kuma Daular Saudiyya, ta taya murna ga sabon Ministan Hajji da Ummara na Saudiyya, Dr. Essam bin Saad bin Saeed bisa sabon matsayin da ya samu.
Cikin wata sanarwar da ta fitar a Litinin da ta gabata a Abuja wadda ta sami sa hannun kodinetanta na ƙasa, Ibrahim Muhammed, cibiyar ta yaba wa Hadimin Masallatan Makka da Madina, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, bisa naɗin da ya yi wa Dr. Essam bin Saad bin Saeed domin jan ragamar harkokin Hajji da Umura a faɗin duniya.
A cewar IHR, “Wannan naɗin abu ne mai matuƙar muhimmanci ga Independent Hajj Reporters da ma ɗaukacin al’ummar Musulmi duba da cewa Dr. Essam bin Saad bin Saeed tsohon ministan labarai ne wanda ya san irin rawar da harkar yaɗa labarai kan taka wajen yaɗawa da ilimantar da al’umma game da harkokin masana’antar Hajji da Umura.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Kafafen yaɗa labarai na da matuƙar tasiri a sha’anin Hajji da Umura musamman kuma a irin wannan lokaci da ake fama da annoba. Akwai buƙatar wayar da kan jama’a game da ƙoƙarin da Saudiyya ke yi wajen yaƙi da cutar korona don amfanin al’ummar Musulmi.”
IHR ta ce a matsayinta na cibiya ɗaya tilo mai yaɗa labarun harkokin Hajji da Umura zalla a yankin Afirka baki ɗaya ta shafinta na inatanet kan adireshi: www.hajjreporters.com, “a shirye Hajj Reporters suke su bada cikakken haɗin kansu ga sabon Ministan Hajji da Umura yayin gudanar da ayyukanmu wajen yi wa maniyyatanmu hidima, tare da addu’ar shiryar Allah wajen yi wa baƙin Mai Rahma aiki.”
Kazalika, IHR ta jinjina wa Ministan Hajji da Umura mai barin gado, Dr. Mohammed Saleh bin Taher Benten dangane da nasarorin da ya samar a masana’antar Hajji da Umura tun bayan da aka naɗa shi a watan Yulin 2016.
Ta ce, “A bayyane yake cewa Dr Saleh Benten ya yi nasarar inganta sha’anin fasahar sadarwa a harkokin Hajji da Umura wanda hakan ya yi tasiri wajen inganta irin kulawar da ake bai wa maniyyata.”
Independent Hajj Reporters, mai wallafa jaridun hajjreporters.com da hajjreportershausa.com da kuma mujallar Hajj Reporters Magazine, cibiya ce mai rajista kuma mai zaman kanta wadda ta haɗa ƙwararrun ‘yan jarida daga sassa daban-daban masu burin faɗakar da maniyyatan Nijeriya game da harkokin Hajji da Umura a faɗin ƙasa.
Duk shekara, cibiyar kan wakilta mambobinta a gida da kuma Saudiyya don su sanya ido tare da yaɗa yadda harkokin Hajji da Umura ke gudana.