CIKAKKEN BAYANI: Yadda za a yi salloli a masallacin ma’aiki a watan Ramadan

0
281

Kamar yadda aka tsara:

– Adadin mutum 60,000 ne za su kasance a cikin masallacin a lokaci guda (45,000 a ciki, 15,000 a waje). Masallatan za su kasance ne a bisa tsarin bada tazara da juna a ciki da wajen masallacin.

– Za a rufe masallacin ma’aikin rabin awa bayan an yi sallar tarawi, sannan sai a sake buɗe shi awanni biyu kafin sallar asuba har sai goman ƙarshe ta Ramadan, inda a sannan ne za a barshi a buɗe ba dare ba rana.

– An tsara cewa Limamai, ma’aikata da masu sallar jana’iza ne kaɗai za su yi sallah a rauda.

– Za a bar masallata su yi sallah a ciki da waje da ma saman rufin masallacin. Za kuma a riƙa duba shi a kai- a kai.

– Kawo yanzu dai ba a sanar da tsare-tsaren da za a yi a kan buɗe baki da ittikafi ba, sai dai ana sa ran sanarwar nan bada daɗewa ba, amma dole sai da sahalewar hukumar lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here