Gwamnatin jihar Legas ta bada tabbaccin za ta yi wa ɗaukacin maniyyatan jihar allurar rigakafin korona kafin soma aikin Hajjin 2021 a ƙasar Saudiyya.
Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Legas, Prince Anofiu Olanrewaju Elegushi shi ne ya bada tabbacin hakan a wajen taron bita shiryawar Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazan na Jihar.
Taron da aka shirya shi musamman domin yi wa jami’an hukumar da malamai da kuma jagororin hajji na jihar, bita kan harkokin Hajji, ya gudana ne a babban zauren taro na masallacin Shamsi Adisa Thomas da ke GRA, Ikeja, in ji wata sanar da ta fito daga hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Taofeek Lawal.
Kwamishinan ya ƙarfafa cewa gwamnantin Gwamna Babajide Olusola Sanwo-Olu za ta yi mai yiwuwa wajen tabbatar da kowane maniyyaci a jihar ya samu allurar, duk da cewa adadin allurar da Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihar ya yi ƙarancin da ba zai wadaci al’ummar jihar ba.
Da yake zurfafa bayani kan taken taron, wato ‘Mafita ga Hajjin 2021 da Shirye-shirye’, ya yi kira ga waɗanda taron ya shafa da su ɗauki damar da suka samu a matsayin wata amana ta yi wa Allah hidima wanda za a tambayi mutum ran gobe ƙiyama.
Daga nan ya buƙace su da su zama nagartattun jakadun jihar tare da ƙoƙarin sauke nauyin da aka ɗora musu gwargwadon hali, saboda a cewarsa aikin da aka ɗora musu aiki ne mai matuƙar muhimmanci, wato kula da jin daɗin maniyyata a gida Nijeriya da kuma a can Saudiyya.
Yayin da ya nuna wa jami’an buƙatar da ke akwai su bai wa juna haɗin kai yayin gudanar da ayyukansu, kwamishinan ya jaddada shirya taron ya zama wajibi domin bai wa jihar damar ci gaba da zama ɗaya daga cikin jijohin sahun gaba a Nijeriya da suka yi fice wajen sha’anin aikin Hajji.
Tun farko da yake jawabi, Sakataren Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai na Legas, Mr. Rahman Ishola, ya yi yabo ga gawamnan jihar Babajide Olusola Sanwo-Olu da mataimakinsa, Dr. Kadri Obafemi Hamzat, bisa ga irin gudunmawar da suke bai wa hukumar.
Ya ƙara da cewa, tare da samun goyon bayansu hukumar za ta aiwatar da ayyukanta daidai da tsarin gwamnatin jihar wajen kula da maniyyatan jihar yadda ya kamata ba tare da la’akari da kowane nau’i na bambanci ba.
Baƙi da suka yi jawabi a wajen taron sun haɗa da; Mai Bai wa Gwamnan Shawara Kan Harkokin Musulunci, Hon. Jebe-Abdullai Ahmad, Dr. Mutiu Olakunle Afariogun na LASUTH, da kuma Mr. Awe Jamiu.