Rigakafin korona ba ta karya azumi, inji Sheikh Sudais

0
1

Shugaban Ma’aikatar kula da Masallatan Harami guda biyu na Makka da Madina, Sheikh Farfesa Dr. Abdul-Rahman bin Abdulaziz Al-Sudais, ya bada fatawar cewar allurar rigakafin korona ba za ta karya azumi ba yayin azumin Ranadan.

Malamin ya bada fatarwar ne daga littafin azumi inda ya yi bayanin hukuncin azumi a shari’ance.

Yayin da yake bada darasin, Imam Sudai ya yi magana kan hukuncin azumi a cikin watan Ramadan. Inda ya nuna cewa duk wanda azuminsa ya karye ta dalilin wani al’amari da aka halasta masa aikatawa cikin azumi, zai rama azumin daga baya.

Daga nan malamin ya bada fatawar cewa sabuwar allurar rigakafin korona ba ta daga cikin jerin abubuwan da suke ɓata azumi a Ramadan.

Haka nan, malamin ya nuna muhimmancin rashin jinkirin ramakon azumin da mutum ya sha ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, inda ya yi ishara da fadar Aisha, (Allah Ya Ƙara Mata Yarda) inda ta tace, “Na kasance ina azumi a Ramadan, duk lokacin da na kasa yin azumin ba na ramawa sai a watan Sha’aban, a wajen Manzon Allah (SAW) sannan idan ya yi jinkirin wajen rama azumi har zuwa wani Ramadan, sai ya azumci sabon Ramadan da ya kama sannan ya rama abin da ya yi saura (na ramakon da bai kammala ba) bayan haka.

A cewar Imam Sudais, idan wanda ake bin bashin azumi ya rasu kafin fara azumin sabon Ramadan, shi kenan babu komai a kansa, saboda ya yi jinkirin ne cikin lokacin da ya rasu ɗin. Amma idan ya rasu bayan sabon Ramadan sannan jinkirin nasa ya kasance saboda lalurar rashin lafiya ko tafiya, nan ma banu komai a kansa. Idan kuwa jinkirin nasa babu wani dalili, wajibi ne sai ya yi kaffara ta hanyar ciyar da mabukaci kulli yaumi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here