NA MUSAMMAN: Alhazan Ummara 20 ƴan Nijeriya sun tashi zuwa Saudiya yau

0
435

Wani rukuni na alhazan Ummara mutum 20 ya tashi daga Nijeriya zuwa Daular Saudi Arebiya domin yin Ummara.

Alhazan sun tashi ne ta filin jirgin sama na Murtala Muhammad a jirgin Ethiopian Airline.

Alhazan sun biya kuɗin yin Ummara ne ta kamfanin Portfolio Travels, Habdat Express Travels, Alfaozan Travels da Alyusuff International Travels.

Hajj Reporters ta rawaito cewa ana sa ran alhazan za su dawo gida Nijeriya ranar 5 ga watan Afrilu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here