Ƴan sandan Saudiya sun kama mutane 2 bisa zargin saida ƙyallaye 7 na zanin Ka’aba

0
459

Jami’an tsaro a Saudi Arebiya sun kama wasu ƴan nahiyar Asiya guda biyu da ƙyallaye 7 na zanin da ake shimfiɗawa Ka’aba (Kiswa) a birnin Makka.

An kama su ne lokacin da ake ƙoƙarin fiton su ta jirgin ruwa zuwa ƙasar waje daga lardin Shasha a Makka, in ji ƴan Sanda.

“Mun kama ƴan Pakistan guda biyu lokacin da suke ƙoƙarin fita da ƙyallaye bakwai daga yadinda ake shimfiɗawa Ka’aba a lardin Shasha,” i ji Ƴan sanda.

Mutanen sun faɗawa masu tuhumar su cewa sun sayi ƙyallayen ne a wajen wani ɗan indiya a layi na 60 kan kuɗi riyal 300.

Yanzu dai an tsare mutanen har sai an gama bincike sai a ga yiwuwar hukuncin da za a yanke musu.

Ana canja zanin Ka’aba ɗin sau ɗaya a shekara a ranar 9 ga watan Zulhijja bayan alhazai sun tafi filin arfa, a wani yanayi na tarbar baƙin Allah washe gari da safe wacce tayi daidai da ranar idin babbar Sallah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here