Jirgin Adashin Gata na Hajji ya sauka a Bauchi

0
428

A yau ne a ka yi gagarumin bikin ƙarshe na ƙaddamar da Adashin Gata na Hajji na shiyya, shiyya a Jihar Bauchi.

Shiyyar ta ƙunshi Hukumomin Kula da Walwalar Alhazai na Jihohin Adamawa, Borno, Bauchi, Gombe da Taraba.

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babban Jami’in Lura da Adashin Gata na Hajji na Hukumar Kula da Jindaɗi da Walwalar Alhazai Musulmai na Jihar Adamawa ta ce ” Sakatare na Din-din-din kuma Shugaban Hukumar, Mallam Salihu Abubakar, wanda kuma mamba ne na kwamitin NAHCON da ta kafa domin su yi nazari kan yiwuwar shirin ya halarci taron tare da Daraktan Ayyuka, Hassan Ali da kuma Jami’in Gudanarwa na shirin, Barkindo Abdullahi Yakubu.

Daga cikin manyan baƙi da suka halarci taron har da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, Shugaban NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here