Hajjin 2021: NAHCON ta umarci Hukumomin Hajji na Jihohi da su yiwa dukkan maniyyata allurar rigakafin corona

0
268

Hukumar Hajji ta Nijeriya (NAHCON) ta ce ta samu wasiƙa daga Hukumar Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) tare da neman NAHCON ta bai wa duka Hukumomin Kula da Walwalar Alhazai na jihohin ƙasar nan 36 su yi wa maniyyatansu allurar rigakafin korona.

A wata takardar sanarwa wadda Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike da Yaɗa Labarai na NAHCON, Sheikh Suleman Momo Imonikhe ya sanya hannu a ranar Lahadi, hukumar ta buƙaci ɗaukacin Hukumomin Kula da Walwalar Alhazai na jihohin ƙasar nan da su hanzarta yi wa baki ɗayan maniyyatansu allurar rigakafin korona.

A cewar NAHCON yin allurar a kan kari hakan zai taimaka wajen samun tazarar makonni biyu da ake buƙata a tsakanin rigakafin farko da na biyu da za a yi kafin lokacin aikin Hajji.

Kwamishinan ya ce ana buƙatar kowane maniyyaci ya shiga ya yi rajistar karɓar allurar da kansa a intanet ta adireshi kamar haka: https//nphcdaict.ng/publicreg.

Tare da cewa, “Waɗanda ba su da zarafin yin rajistar ta intanet za a samar da wani tsarin da zai ba su damar yin hakan cikin sauƙi a cibiyoyin bada allurar.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here