Shugaban NAHCON ya yabawa Ganduje kan Adashin Gata na Hajji

0
215

…Ya kuma yaba masa kan bawa hukumar Hajji ta jihar na’ura mai ƙwaƙwalwa

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Bar. Zikrullah Kunle Hassan ya yabawa Hukumar kula da Walwala da Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano a bisa zama kan gaba wajen wacce tafi yawan waɗan da suke yin rijista domin tsarin Adashin Gata na Hajji.

Kunle ya yi yabon ne lokacin da yake ganawa da Shugabannin Hukumomin Kula da Walwalar Alhazai na Jihohi a Shalkwatar hukumar da ke Abuja.

Wata majiya daga waɗanda suka halarci ganawar ta shaidawa Hajj Reporters cewa “Shugaban NAHCON ɗin ya nuna jin daɗi da godiya gwamnatin Jihar Kano da ta samar da na’ura mai ƙwaƙwalwa har 47 ga hukumar da kuma na’urar yin katin ɗan ƙasa da kuma sahalewar da gwamnatin tayi na bawa hukumar mota mai cin mutum 18 domin sauƙaƙa hada-hada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here