Wani rukunin na alhazai ƴan Nijeriya ya tashi daga filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Jihar Legas zuwa Daular Saudi Arebiya.
Alhazan sun tashi ne ta kamfanunuwan Portfolio Travels, Alfirdaos Hajj da Umrah Services Ltd, Zaatim Travels, Alyusuff international da Alatiq Travels, inda ake sa ran za su dawo a ranar 12 ga watan Afrilu.
Shugaban Alfirdaos Hajj and Umrah services Ltd, Imam Ekundayo Abdullateef ya shaidawa Hajj Reporters cewa a yanzu haka alhazan na Saudi Arebiya.