Hajjin 2021: An fara yiwa maniyyata rigakafin korona a Jihar Nassarawa

0
254

Hukumar Kula da Jindaɗ da Walwalar Alhazai ta Jihar Nassarawa ta ce ta fara yiwa maniyyatan Hajjin 2021 allurar rigakafin COVID-19, wacce aka fi sani da korona.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, AbdulRazak Muhammad, hukumar ta ce za a gudanar da yin allurar rigakafin ne tsawon kwanaki biyu.

Yayin ziyara zuwa ɗaya daga cikin cibiyoyin yin rigakafin, Shugaban Hukumar, Mallam Idris Ahmad Almakura ya yi kira ga maniyyatan da su kai kan su a yi musu rigakafin, inda ya ƙara da cewa hukumar ta samar da cibiyoyin yin allurar a Ƙananan Hukumomin Lafiya, Keffi da Akwanga.

Almakura ya kuma tunatar da maniyyatan cewa yin rigakafin na ɗaya daga cikin manyan sharuɗɗa na zuwa Hajjin bana, inda ya jaddada ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen samar da allurar a karo na biyu a lokacin da ya dace.

Ya kuma yabawa gwamnan Jihar Nassarawa Abdullahi Sule da Hukumar Lafiya a Matakin Farko abisa taimakawa hukumar ta samu alluran rigakafin ba tare da matsala ba.

Sannan shugaban hukumar ya kaiwa Sarkin Nassarawa, Mai-martaba Sarki Jibrin Usman ziyara, inda Sarkin ya yabawa hukumar domin samar da cibiyar yin rigakafin a Nassarawa, inda ya ce hakan ya sauƙaƙawa mutane wahala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here