Hukumar Hajji ta fara allurar rigakafin corona ga maniyyata, amma ta soma da jami’an ta

0
1

Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta Jihar Kano, ta ce ta ƙaddamar da shirin allurar rigakafin cutar korona ga maniyyatan Hajjin 2021 a jihar inda ta soma bada allurar ta kan ma’aikatanta.

A wata sanarwa da ta fitar ta hannun jami’arta ta hulda da jama’a, Hadiza Abbas Sunusi, hukumar ta ce ta soma gudanar da shirin ne a Larabar da ta gabata inda aka buɗe fagen yin allurar da fara yi wa Sakataren Hukumar, Muhammad Abba Dambatta.

A cewar Sakataren, an ƙaddamar da shirin yin allurar ne domin cika sharaɗin da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayar a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen Hajjin bana.

Muhammad Abba Dambatta ya bayyana cewa hukumar tasu tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Lifiya ta Jihar, sun kammala dukkan tsare-tsaren da suka kamata da zummar cim ma manufar da aka sa a gaba.

Tare da cewa hukumar za ta tabbatar da ɗaukacin maniyyatan an samu yi musu rigakafin Oxford-AstraZeneca a cibiyoyin da aka shirya gudanar da shirin.

Dabbatta ya yi nuni da cewa yayin wani taron da suka gudanar a baya-bayan nan, Shugaban Hukumar Hajji na Ƙasa, Barrister Zikirullah Kunle Hassan, ya yaba da ƙoaƙarin Gwamnan Kano da ya taiamaka wa hukumar da wasu kayayyakin aiki da suka haɗa da na’urar binciko lambar BVN, ƙananan kwamfuta guda 47, da mota bas guda uku.

Haka nan, ya yaba da irin nasarorin da aka samu kawo yanzu a Jihar Kano dangane da Shirin Adashin Gata don tanadin zuwa aikin Hajji.

Daga nan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga ɗaukacin maniyyata da su tabbatar da sun yi allurar rigakafin korona, saboda a cewarsa babu wani maniyyaci da za a bari ya tafi Hajji ba tare da ya yi allurar ba.

Sa’ilin da yake jawabi a madadin masu ruwa da tsaki na hukumar, Shugaban Hukumar Alhazai na Kano, Farfesa Abdallah Saleh Pakistan, ya buƙaci dukkan maniyyatan jihar da su bada haɗin kai ga shirin yin rigakafi tun da abu ne da bai saɓa wa Musulunci ba.

Farfesa Pakistan ya yi amfani da wasu ayoyin Alƙur’ani da Hadisai wajen nuna muhimmancin neman magani yayin da aka samu ɓarkewar wata annoba. Tare da bai wa al’umma shawara, musamman ma maniyyata, da su karɓi allurar da kyakkyawar niyya suna masu yaƙinin cewa babu abin da zai cutar da lafiyarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here