Hukumar Kula da Walwala da Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta fara yiwa ma’aikatan ta da kuma maniyyata aikin Hajjin bana allurar rigakafin COVID-19, wacce aka fi sani da korona.
Ana gudanar rigakafin ne a sakatariyar Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu, mai laƙabin Magajin Gari a jihar ta Kaduna.
Wakilin mu da ya ke gurin ya rawaito ce shugabar hukumar ta riƙon ƙwarya, Hajiya Hanatu Zailani da kuma Shugaban shashin aikace-aikace na riƙon ƙwarya, Alh. Abubakar Alhassan da wasu daga cikin maniyyatan duk an yi musu allurar.
Wasu daga cikin maniyyatan sun nuna gansuwar su da yadda ake gudanar da allurar cikin sauƙi.
“Na yi farin ciki saboda na tsorata kafin a yi min allurar, amma yanzu an yi min allurar. Kaga kenan a shirye nake da na je Hajji idan har za a yi shi a bana,” a ta bakin Bala Muhammed, maniyyaci da aka yiwa rijista daga Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa.