Zamu ƙwace kujerar Hajji ga duk maniyyacin da bai yi rigakafin korona kafin Alhamis ba- Abuja

0
384

Hukumar Kula da Walwala da Jin daɗin Alhazai Musulmai ta Abuja ta shawarci maniyyatan da suka yi rijistar Hajjin 2021 da ba su yi allurar rigakafin korona ba da su garzaya a yi musu kafin Alhamis, 8 ga watan Afrilu ko su rasa kujerar Hajjin su.

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Mallam Aliyu ta ce a ranar Alhamis ɗin za a kammala zango na farko na rigakafin.

Aliyu ya ƙara da cewa “duk maniyyatan Hajjin 2021 su je a yi musu allurar rigakafin kafin ranar a shelkwatar hukumar Hajji ta Abuja”.

Ya ƙara da cewa duk maniyyacin da bai je an yi masa kafin ranar ba to zai iya rasa kujerar sa domin allurar na ɗaya daga cikin sharuɗɗan zuwa Hajji bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here