Ramadan, Hanyar Fita Daga Cikin Kunci Da Damuwa!!!

0
201

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Alhamdulillah, muna kara godiya ga Allah bisa ni’imominsa da baiwarsa a gare mu. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabin mu Muhammadu (SAW).

Ya Allah, muna rokon ka a koda yaushe, da kayi muna mai kyau.

Ya Allah, ka taimake mu. Ya Allah, ka bamu nasara a rayuwar mu, da cikin dukkanin al’amurran mu. Ya Allah, ka tsaya muna, ka dafa muna, kayi muna maganin duk wani abinda ya dame mu, ko yafi karfin mu.

Ya Allah, watan Ramadan yazo. Ya Allah, yadda ka dauke hammu da gammu da yunwa da duk wata irin damuwa, ga alummar Annabi Muhammad (SAW), a lokacin annobar korona da lockdown, Ya Allah, ka dubi wannan al’ummah da irin wannan Rahamar a wannan lokaci da zamu shiga na Ramadan. Domin a gaskiya al’ummah suna cikin wani hali, musamman talakawa da mabukata.

Mafi yawan mutane basu da kudi, ‘Yan kasuwar mu babu ciniki, kai wasu ma jarin ya karye baki daya. Ma’aikata babu wadataccen albashi, kai a wasu jihohin ma babu albashin kwata-kwata. Albashi ya zama bashi a gare su.

Ya Allah, dukkanin mu, kowa kazo masa da ludufin ka, ta inda bai yi zato ko tsammani ba.

Ya Allah, bawan ka, Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II. Ya Allah, wannan bawa naka yana iya kokarin sa wurin taimakon talakawa da sauran bayin Allah. Wanda har yanzu da nike wannan rubutu, yana kan iya kokarin sa, ba daina wa yayi ba.

Ya Allah, an raba jama’ar jihar Kano, da sauran talakawa da farin cikin su. Ya Allah, wannan bawa naka, Sarki Muhammadu Sanusi II, idan Ramadan da Sallah sun zo, taimakon bayin Allah yake yi, babu ji babu gani. Ya Allah, duk wanda yake da hannu cikin raba talakawa da farin cikin su, Ya Allah, ka raba shi da farin ciki da kwanciyar hankali na har abada.

Akwai bayin Allah masu hali, masu arziki, da su ma suke iya bakin kokarin su, wurin taimakon talakawa da bayin Allah, musamman a lokacin Ramadan, ina rokon Allah ya taimake su, ya basu karfin gwiwa da juriyar ci gaba da wannan aiki. Wadanda ba sa taimakawa kuwa, ina rokon Allah ya basu iko, da karfin halin taimakawa, domin a gaskiya, al’ummah tana cikin wani hali. Kuma wallahi ba zaka taba yin farin ciki ba har sai ka sa bayin Allah cikin farin ciki. Kuma ba zaka taba fita daga cikin damuwa ko kunci ba, har sai ka fitar da bayin Allah daga cikin damuwa da kuncin rayuwa!

Ya zama wajibi gwamnatocin mu, tun daga gwamnatin tarayya, har na jihohi, har na kananan hukumomi, da sauran ‘yan siyasa, da sanatoci, da ‘yan majalisun wakilai na tarayya, da ministoci, da ‘yan majalisun jihohi, da sarakunan mu iyayen al’ummah, da sauran masu hali, su taimakawa bayin Allah, talakawa, musamman cikin wannan wata na Ramadana, da kuma hidimar Sallah mai zuwa.

Ina mai yi maku rantsuwa da Allah, Al’ummar Annabi Muhammad (SAW) suna cikin wani hali, ku taimaka masu. Ku sani, taimakon su yana dauke fushin Allah, tsaro ya samu, a samu kwanciyar hankali, da zaman lafiya cikin al’ummah. Ba ka da wani wayo ko dabara da zaka iya yiwa mutumin da yake jin yunwa, ko kuma yake cikin kuncin rayuwa. Don ba zai ma saurareka ba wallahi! Sannan a daya gefen, duk wani mugu da ya tuntube shi da shiga wata mummunar hanya, wallahi shiga zai yi, indai har zai samu dan abun biyan bukatar rayuwa.

Ya Allah don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), Ya Allah, muna tawassuli da ayukkan mu kyawawa, ka kara jefa duk wani makiyin talakawa cikin zulumi da tashin hankali da damuwa, bisa cin amanar talakawa da yake yi, ko wanene shi!

Ya Allah, matayen mu, wadanda basu da aure, Allah ka basu mazaje nagari, masu addini, masu kyawawan halaye, masu dattaku da kamala. Ya Allah, ka sanya hijabi tsakanin su da fasikan mutane, masu bata masu rayuwa.

Mazajen mu da matayen mu masu aure kuwa, Ya Allah ka rike masu auren su cikin nasara da albarka. Ya Allah, ka kula masu da zuriar da ka albarkace su da ita.

Ya Allah, ka dubi kasar mu Najeriya, da jihohin mu na arewa da idon rahamar ka da tausayin ka. Ya Allah, ka dauke muna halin rashin tsaro da fitintinu da tashin hankali. Ya Allah, kayi muna jagoranci. Ya Allah, ka taimaki kasar nan da shugabanni na gari daga ko’ina suke. Ya Allah, ka biya wa kowa bukatunsa na alkhairi.

اللهم احسن عاقبتنا فى الامور كلها واجرنا من خزى الدنيا وعذاب الاخرة، اللهم اجعلنا منك فى عياذ منيع وحرز حصين من جميع خلقك حتى تبلغنا اجلنا معافى، اللهم من رامنا فرمه، ومن كادنا فكده، ومن قصدنا بسوء فخذه اخذ عزيز مقتدر، ولا تمهله، وحل بيننا وبينه بسردقات عظمتك وقهرك يارب العالمين. اله البرايا العدل ذا البطش فاقهرن جميع العدى ولتكفنا خير راحم بجاه سيدنا محمد المبعوث رحمة للعالمين.

Mu cika da Fatiha, ya Allah, ka amsa, amin.

Daga dan uwanku, Imam Murtadha Gusau – 08038289761

Laraba, 07/04/2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here