Hajjin 2021: An ƙaddamar da yin rigakafin korona ga maniyyata a Katsina

0
343

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina, Alh Suleman Nuhu Kuki ya ƙaddamar da yin allurar rigafin cutar Korona ga maniyatan aikin Hajjin bana .

Shugaban hukumar ya ce wajibi ne ga duk wanda zaije Hajjin bana a tabbatar anyi masa wannan allura kamar yadda umurnin yazo daga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON).

Ya ƙara da cewa, hakan yasa abisa umurni da amincewar Gwamna Aminu Bello Masari za a fara yiwa maniyatan da suka fara biyan kuɗin aikin Hajjin na bana.

Kuki ya bayyana cewa za a fara yin allurar rigakafin ne gobe a shiyar Katsina, Daura da Funtua.

Bayan gama jawabi, take aka fara da yiwa Shugaban hukumar allurar tare da duk ma’aikatan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here