Hajjin 2021: Za a yiwa maniyyatan Ogun rigakafin korona ran Asabar da Lahadi

0
1

Shugaban Hukumar Kula da Jin Daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Ogun, Alhaji Salau Dauda Babatunde ya ce maniyyata a jihar za su ɗauki allurar rigakafin COVID-19, wacce aka fi sani da korona a ranakun Asabar da Lahadi.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa ranar Laraba, inda ya ƙara bayyana cewa gwamnatin jihar ce ta sahale da a yiwa maniyyatan allurar rigakafin.

“Gwamnatin Jihar Ogun ta sahale da a yiwa maniyyatan Hajjin bana allurar rigakafin korona kamar yadda Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta umarta a wani sharaɗi na zuwa aikin Hajjin bana,” in ji sanarwar.

Babatunde ya sanar da cewa za a yi rigakafin ne a ranar Asabar, 10 ga watan Afrilu, da Lahadi, 11 ga wata, inda yayi kira ga maniyyatan da su halarci sakateriyar hukumar, a gini mai lamba B, Oke-Mosa, Abeokuta, sannan su tafi da shaidar biyan kuɗin Hajji domin tabbatar da maniyyaci.

Sannan ya sanar da cewa waɗanda aka riga a ka yiwa rigakafin a ƙananan hukumomin su sai su kawo katin da ake bayarwa idan an yiwa mutum allurar domin shigar da su a cikin kundin bayanan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here