Ma’aikatar Ayyukan Cigaba da Nazarin Ayyukan Fasaha (engineering study) ta bada tabbacin cewa a watan Ramadana, za a buɗe yankuna da guraren da aka tanadarwa alhazan Ummara da masallata a sabbin guraren da aka ƙara domin faɗaɗa Masallacin Harami.
Tabbacin ya fito ne daga bakin Babban Daraktan fannin Ayyukan Cigaba da Nazarin Ayyukan Fasaha, Sultan Al-Qurashi, da kuma Babban Daraktan Kula da Gudanar da Ayyukan Cigaba, Injiniya Ammar Al-Ahmadi, waɗan da suka wakilcin Babban Ofishin Tafikar da Ayyukan Gine-gine na ma’aikatar kuɗi, da kuma ɗan kwangilar da ya aiwatar da aikin (Saudi Bin Laden Group) a yayin ziyarar duba aikin.
A yayin ziyarar, an yi garambawul a guraben da aka tanadarwa masallata da kuma hanyoyin wucewa domin hana cinkoso, da ma ɗaukacin sauran ayyuka domin a tabbata kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Injiniya Sultan Al-Qurashi ya jaddada cewa duk wannan ayyuka da tsare-tsaren da aka yi bisa hikima da fasaha ta zamani, tare da haɗin gwiwa da duk hukumomin da suka dace, an yi ne domin baƙin Allah su sakata su wala da kuma irin gagarumin ƙoƙari da aka yi na faɗaɗa Harami da ƙasar ta yi.