NA NUSAMMAN: Rukunin farko na alhazan Ummarar Ramadana ƴan Nijeriya sun sauka a Saudiya

0
421

Rukunin farko na alhazan Ummarar azumin watan Ramadana ƴan Nijeriya su 15 sun sauka a Saudi Arebiya.

Hajj Reporters ta rawaito cewa an ga alhazan suna ta ibada a cikin Raudah, masallacin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, inda daga bisani suka wuce Makkah domin yin Ummara.

Alhazan, waɗanda suka tafi ta kamfanin Raudah Travel and Tour Ltd da ke Kano za su fara yin Azumin watan Ramadana kafin su dawo gida Nijeriya.

Ɗaya daga cikin alhazan, Aminu Ibrahim, ya bayyana farin cikin sa game da yadda za su fara yin azumi a Saudiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here