Ma’aikatar harkokin Hajji da Ummara ta ƙasar Saudi Arebiya a ranar Lahadi ta bayyana cewa sau ɗaya tak alhaji ko hajiya za ta yi Ummara a cikin watan Ramadana. Wannan dokar an saka ta ne domin a bawa ɗumbin al’umma su samu damar aikata ibadar.
A ranar Lahadi ne Ma’aikatar harakokin Hajji da Ummara ta fara bada takardar sahalewa a yi ummara da salloli a Harami, kuma a mako-mako za ta riƙa bada sahalewar.
Ta kuma ce za a samu shaidar sahalewar ne ta manhajar “Eatmarna” ko ta hukumar lafiya mai suna “Tawakalana”.
Shaidar sahalewar za ta fito ne kaɗai ga wanda bayanin sa ya nuna “immune” wato kariya a kan manhajar Tawakalana. Shima bayanin “immune” ɗin kashi uku ne; immune kawai, Immune bayan an warke da kuma immune na ɗaukar allura na farko.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa shaidar sahalewar da a ka bayar domin sallar isha, shi za a bayar domin sallar Taraweeh.