HAJJIN 2021: Maniyyata 2,837 aka yiwa rigakafin korona

0
1

Hukumar Kula da Jindaɗi da Walwalar Alhazai Musulmai ta Jihar Kaduna ta ce maniyyata 2,837 ne aka yiwa allurar rigakafin COVID-19, wato korona domin Hajjin 2021.

Shugabar hukumar ta riƙon ƙwarya, Hannatu Zailani, wacce ta bayyana hakan ga manema labarai, ta ce an fara gudanar da rigakafin ne a ranar 6 ga watan Afrilu.

Shugabar ta bayyana cewa Jihar Kaduna na da kujerar Hajji sama ga sama da maniyyata 4,000 a bana 2,837 ne suka je aka yi musu rigakafin a gaba ɗaya Ƙananan Hukumomi 23 da ke jihar, inda ta ƙara da cewa a cikin makon nan za a kammala yin rigakafin.

Ta kuma yi bayani cewa ana gudanar da allurar rigakafin a bisa umarni daga Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON.

Shugabar ta jaddada cewa duk wani maniyyaci ba zai tafi aikin Hajji ba har sai an yi masa rigakafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here