Ku tabbata kun karrama alhazan Ummara, a kula da lafiyar su, Sarki Salman ya bada umarni

0
1

Hadimin Masallatan Harami Guda Biyu, Sarki Salman na Saudi Arebiya ya bawa hukumomin da suka dace umarnin bawa alhazan Ummara cikakkiyar kulawa da kuma tabbatar da sun samu kwanciyar, kula da lafiyar su da kuma tsaro a cikin watan Ramadana mai albarka.

Sarki Salman ya bada umarnin ne a ranar Talata yayin da ya jagoranci ganawar jami’an gwamnati ta yanar gizo-gizo.

A yayin ganawar, Hadimin Masallatan Harami Guda Biyu ɗin ya godewa Allah da Ya bawa musulmai baiwa iri iri da suka haɗa da watan Ramadana, watan Ƙur’ani, rahama da yafiya.

Ya kuma godewa ɗaukacin shugabanni, baƙi da kuma ƴan ƙasa abisa addu’o’i da fatan alheri da suka riƙa yiwa kasar sakamakon zagayowar wata mai alfarma.

Sarkin yayi addu’a a kan Allah Ya kaɓi ibadu Ya kuma kawo ƙarshen annobar COVID-19, wacce aka fi sani da korona.

A wata sanarwa da ya aikewa Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya, Ministan Yaɗa Labarai, Majid Al-Qasabi ya bayyana cewa a ganawar, jami’an gwamnatin sun sake yin duba a kan saurin farfaɗowar tattalin arziki da cigaba da aka samu a dukkan matakai a ƙasar da ya zo daidai da tsare-tsare da shirye-shirye na 2030, da kuma sauran batutuwa a ɓangaren harkokin kuɗaɗen shiga na ƙasar.

An tattauna batutuwa masu muhimmanci game da shirye-shiryen da kasar ke yi na cigaba da farfaɗo da tattalin arziki nan da shekaru masu yawa a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here