A matsayin wani mataki na cika umarnin da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta bayar dangane da shirin Hajjin 2021, jihar Cross River ta ce ta kammala yi wa jami’an gudanarwa na Hukumar Kula da Walwalar Maniyyatan Jihar da ma su kansu maniyyatan bana, allurar rigakafin cutar korona.
Shugaban Hukumar kula da jin daɗin Musulmi maniyyata na jihar, Alh. Rabilu Abdullahi Maimaje ne ya shaida wa HAJJ REPORTERS hakan, tare da cewa “Jihar ta shirya wa aikin Hajjin 2021”.
A cewar Alh. Rabilu Abdullahi, a ranar 14 ga Afrilu, 2021 ta soma shirin bada allurar inda a yanzu ta ce ta kammala komai daidai da umarnin Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON)
Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne NAHCON ta bada umarni kan jihohi su hanzarta yi wa maniyyatansu rigakafin korona domin cika sahruɗɗan aikin Hajjin 2021.