Dole alhazan Ummara baƙi su nuna shaidar yin rigakafin korona- Hukumar Hajji ta Saudiya

0
406

Hukumar Hajji da Ummara ta ƙasar Saudi Arebiya ta sanar da cewa dole ne sai alhazan Ummara da suka zo daga ƙasashen waje sun nuna shaidar cewa an yi musu allurar rigakafin COVID-19 a ƙasashen su.

Kakakin hukumar, Eng. Hisham Saeed ne ya bayyana hakan yayin amsa tambaya daga Okaz/Saudi Gazette a taron manema labarai na haɗin gwiwa ran Lahadi, domin bada bayanai a kan halin da ake ciki kan annobar korona.

Saeed ya cigaba da bayyana sabbin tsare-tsaren da aka tanadarwa alhazan Ummara da suka zo daga wasu ƙasashe a watan Ramadana, inda ya ce matsayin lafiyar alhazan ta ta’allaƙa ne da manhajar Tawakalana ta Hukumar Lafiya ta ƙasar.

Daga cikin tsare-tsaren, alhazai baƙi, waɗanda suka zo da shaidar yin rigakafin su za su zarce zuwa ɗaya daga cikin cibiyoyin kulawa (inaya) a garin Makkah domin tantance sahihancin shaidar.

Bayan kammala wannan matakan, sai cibiyar ta sanya rana da lokaci da alhaji zai yi Ummara da sallah a masallacin Harami mai tsarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here