Malamai sun yi addu’o’i kan aikin Hajjin 2021

0
494

Daga Jabiru Hassan, Kano

Malamai masu gabatar da tafsir na watan Ramadan sun yi addu’oi na musamman domin ganin an gudanar da aikin Hajji a bana cikin nasara, tareda fatan ganin karshen dukkanin wani abu da ka iya kawo tsaiko a shirin da ake yi na ganin an cimma nasarorin da ake bukata.

Wakilin mu wanda ya halarci wasu masallatan da ake tafsir, ya ruwaito cewa dukkanin malaman sun shirya addu’o’i na neman amincin Allah kan harkar Hajjin bana.

Malaman sun kuma yi fatan cewa za a ci gaba da gudanar da aikin Hajji da Umara duk shekara bayan annobar Korona wadda ta zamto barazana a fadin duniya baki daya.

Ustaz Aliyu mai Almajirai Kwa, wanda yake gabatar da tafsir a babban masallacin juma’a na Kwa, ya jagoranci addu’a kan Hajjin bana tareda yin kira ga daukacin musulmin duniya da su kara yin addu’oi in domin samun nasarar ganin anyi aikin Hajji mai albarka a wannan shekara.

Shima na’ibin limamin masallacin garin Yar Gudau sheikh Sani Muhammad ya yi doguwar fadakarwa kan rubanya addu’oi na dorewar kwanciyar hankali a suniya ta yadda al’umar musulmi zasu ci gaba da ziyartar kasa mai tsarki domin aikin Hajji da Umara batare da samun wata matsala ba, tareda fatan cewa za’a ci gaba da gudanar da shirye-shirye kan aikin Hajji kamar yadda aka saba.

Daga karshe, dukkanin limamai na addinin musulunci da suka yi addu’oi sun yabawa hukumar kula da aikin Hajji ta kasa, NAHCON da hukumomin kula da aikin Hajji na jihohi da dukkanin masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umara tareda yin fatan alheri ga kungiyar Independent Hajj Reporters.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here