Ma’aikatan da ke lura da sha’anin Ɗawafi a Ka’aba sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da gagarumar damar da suka samu wajen yi wa maniyyata da sauran jama’a masu gabatar da ibada hidima a kusa da Ka’aba a wannan wata na Ramadan mai cike da albarka.
Ma’aikatan sun bayyana yanayin ayyukan nasu da suka haɗa da lura da zirga-zirgar jama’a, kula da ɓangaren masu fama da nakasa, tabbatar da bada tazara a tsakanin masu ibada da sauransu.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan, Rashid Al-Zahrani, ya bayyana ra’ayinsa inda ya ce, “Ba zan iya bayyana irin daɗin da nake ji yayin da nake aikina kusa da Ka’aba ba, wannan wani farin ciki ne da zai ci gaba da wanzuwa a raina muddin ina raye.
“Ina ɗaya daga cikin waɗanda suka samu zarafin yi wa maniyyata da masu ibada hidima sakamakon annobar da duniya ke fama da ita wanda ke nuni da irin tsananin sha’awar da yake da ita ga irin tallafi mara iyaka da masallatan harami biyu suke samu da kuma tsarin hidindimun Makassedhma a zamanin sarakunan Saudiyya.”
Shi ma ma’aikaci Majed Al Fellit, wanda ke aikin kula da motocin raba ruwan Zamzam, ya ce shi da abokan aikinsa sukan raba wa jama’a euwan Zamzam a ƙofar shiga da fita Mataf daidai da ingantattun tsare-tsaren da hukuma ta samar domin cika sharuɗɗan kariya. Inda aka tsara motocin daidai da yadda za su riƙa shiga da fita wuraren da ake buƙata don raba ruwan Zamzam.
Ma’a’ikatan da ke da haƙƙin raba ruwan Zamzam sun bayyana jin daɗinsu game da damar da suka samu na yin aiki kusa da Ka’aba, inda sukan yi wa maniyyata da sauran jama’a da ke gabatar da ibada hidima.
Ya ce tsarin aikin da aka shimfiɗa musu, na ƙarfafa musu wajen yi wa baƙin Mai Rahma hidima yadda ya kamata a wannan wata mai alfarma.