Majalisar Ƙoli ta kula da harkokin Masallacin Ka’aba da Masallacin Annabi (SAW) a ƙasar Saudiyya, ta ƙaddamar da shirin jigilar dattawa da nakasassu masu ibada a sassan masallatan biyu.
Fadar shugaban kula da masallatan ta ƙaddamar da wannan tsari ne domin sauƙaƙa wa waɗanda aka samar da shirin domin su zirga-zirga yayin da suke ibada a masallatan.