Saudiya ta hana ƙananan yara yin Ummara a watan Ramadana

0
420

Ma’aikatar harkokin Hajji da Ummara ta Ƙasar Saudi Arebiya ta jaddada matakin da ta ɗauka na hana iyaye zuwa da yara ƙanana aikin Ummara da yin salloli a masallacin Harami a cikin watan Ramadana.

Ma’aikatar ta bayyana cewa matakin na ɗaya daga cikin sabbin tsare-tsaren da ta sanar da su wanda sune za su zama tsani na a bada shaidar sahalewar yin Ummara da sallah a masallacin Harami a watan Ramadana mai tsarki.

Tun a baya dama ma’aikatar ta bayyana cewa ƴan shekaru 18 zuwa 70 ne na iya kewayen ƙasar za a bari su yi Ummara daidai da sharuɗɗan da Hukumar Lafiya ta ƙasar ta gindaya.

A tuna cewa tun a baya dama ma’aikatar ta bayyana cewa tanadar lokacin yin salla a Harami za a yi kuma iya na rana ɗaya, inda ta ƙara da cewa idan mutum ya tanadi yin sallar kuma bai samu damar zuwa ba, to neman da yayi ya san ruwa, sai dai ya sake aikawa da neman a tanadar masa lokacin yin salla a babban masallacin mai alfarma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here