Shirye-shiryen Hajjin 2021: Ina aka kwana, ina za a tashi

0
540

Daga Ibrahim Muhammed (Kodinetan
Independent Hajj Reporters na Ƙasa)

Anya ko Hajjin bana zai gudana kuwa, ko kuwa Hajjin 2021 zai gudana ba tare da maniyyatan ƙasashen ƙetare sun samu halarta ba kamar yadda ya auku a 2020?

Idan ya tabbata cewa Hajjin 2021 zai gudana, to, yaya yanayin kason gurbin maniyyatan da za a bai wa ƙasashe zai kasance? Mene ne zai zama ma’aunin shekaru da kuma allurar rigakafin cutar korona, abubuwa masu muhimmanci da za su tantance adadin maniyyatan da za su yi Hajjin bana?

Waɗannan su ne tambayoyin da maniyyata da masu faɗa a ji haɗa da sauran jama’a sukan yi wa Hajj Reporters ta kafafen sadarwa na zamani da wasunsu.

A halin da ake ciki, shirye-shiryen Hajji a ƙasashe masu zuwa Hajji na nan a tsari daban-daban. Yayin da wasu ƙasashe suka riƙi tsarin ‘mu jira mu gani’, wasu ƙasashen kuwa tsarin ‘zauna da shirinka’ suka ɗauka.’ Sai kuma tsarin ‘tsara, shirya sannan ka jira’ da wasu ƙashe suka runguma.

A ƙarshen lamari, waɗannan tsare-tsaren za zu tabbatar da ƙasashen da za su iya kimtsa wa Hajjin na bana kafin lokacin da Ma’aikatar Hajji da Umura za ta bada sanarwar buɗe hanyar gudanar da Hajjin 2021wanda alamu ke nuni mai yiwuwa a bada sanarwar ya zuwa goman ƙarshe na Ramadan.

Bisa la’akari da kalandar Musulunci ta Saudiyya, an yi hasashen Ranar Arfa ta faɗa 19 ko 20 ga Yuli, wato kimanin kwanaki 80 daga yanzu. Sannan soma jigilar maniyyata da sauransu za a aiwatar da hakan ne nan da kwana 60. Don haka tun yanzu ya kamata mu kimtsa saboda kauce wa fafe gora ranar tafiya.

Sai dai a baya-bayan nan wasu muhimman alamu game da harkokin Hajji da Umura a Saudiyya, sun nuna buƙatar da ke akwai masu jagorancin aikin Hajji su fitar da tsare-tsaren yadda za su gudanar da ayyukan Hajji na 2021. Waɗannan alamu kuwa sun haɗa da; tallafin da Sarki Salman ya bai wa fannin Hajji da Umura, naɗa sabon Ministan Hajji da Umura da dai sauransu.

Wata alamar har wa yau ita ce, ƙara yawan shekaru na maniyyata Umura na cikin gida daga 60 zuwa 70, sai kuma furucin da Ma’aikatar Lafiyar Ƙasar Saudiyya ta yi inda ta ce duk maniyyatan ƙasa da ƙasa da ke sha’awar yin Umura su tabbatar sun yi allurar rigakafin korona, ga kuma batun faɗaɗa cibiyoyin hutu na maniyyata, faɗaɗa masallatan Makka da Madina, bada damar yin Umura ga maniyyata daga ƙetare a Ramadan da sauransu.

Duba da duka bayanan da suka gabata, abin tambaya a nan bai rataya kan ko Hajjin bana zai yiwu, ko kuwa za a bada dama ga maniyyatan ƙasa da ƙasa su yi Hajji, a’a, amma yaya tsadar take, yaya yanayin sharuɗɗan, sai kuma adadin maniyyata da za a bari su aiwatar da Hajjin?

Da yawan masu ruwa da tsaki a harkar Hajji da Umura waɗanda ke da yaƙinin ina da wadatattun bayanai sun yi shakkun yiwuwar Hajjin bana saboda rashin rattaba hannu a yarjejeniyar fahimtar juna kamar yadda aka saba tsakanin masu faɗa a ji kan saha’anin Hajji da Ma’aikatar Hajji da Umura ta Saudiyya.

Da a ce da buƙatar sanya wa yarjejeniyar hannu da an yi hakan tun kafin Ramadan, kodayake dai akwai bayanai da ke nuni da cewa sanya wa yarjejeniyar hannu ba ya daga cikin tsarin Hajjin 2021.

A bisa al’ada, albarkacin yarjejeniyar akan san ƙasashen da za su yi Hajji a shekara da kuma tsare-tsaren da aka shimfiɗa game Hajjin daga farko har zuwa kammalawa.

Ga dukkan alamu, Hajjin wannan shekara zai gudana ne daidai da dokokin yaƙi da cutar korona wanda ya hana haɗa cinkoson jama’a. Wanda hakan ke nufin ƙasashe ba za su yi wani kashe jiki ba kan abin da ya shafi masaukin maniyyata, abincinsu, jigilarsu, buƙatu masu alaƙa da kula lafiya da sauransu.

Mai yiwuwa Ma’aikatar Lafiya ta Sauddiyya ta farfaɗo da yarjejeniyar da suka cim ma da jagororin Hajji a 2020 da aka sanya wa hannu tare da kamfanonin Hajji na ƙasar.

Adadin Maniyyata da Ake Buƙata:

Babban abin ji yanzu shi ne yawan gurbin maniyyata da za a bai wa ƙasashen da ke da maniyyata, ko kuma a taƙaice a ce: Mene ne adadin kujerun Hajjin da za a bai wa kowace ƙasa a Hajjin bana? ‘Yar manuniyar da aka samu dangane da haka shi ne furucin da Ministan Harkokin Addini na ƙasar Pakistan, Sahibzada Noor-ur-Haq Qadri, ya yi kwanan baya.

Sa’ilin da yake zantawa da manema labarai, ministan ya furta cewa maniyyatan Pakistan 40,000 zuwa 50,000 ne za a bai wa damar sauke farali a wannan shekarar. Har ya ƙara da cewa Hajjin 2021 zai gudana ne cikin yanayi na musamman mai cike da dokoki da sharuɗɗa da suka haɗa da la’akari da yawan shekarun maniyyata.

Baya ga rigakafin korona kashi biyu da aka wajabta wa maniyyata su yi, ministan ya ce mai yiwuwa maniyyata ‘yan ƙasa da shekara 20 da kuma ‘yan sama da shekara 50 ba za a bari su yi Hajjin bana ba. Sai dai, yana da kyau a sani cewa kalaman ministan ba wata sanarwa ce ba daga Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya, amma Minista Sahibzada Noor-ur-Haq Qadri na ɗaya daga cikin manyan jami’an da Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya ta yarda da su. Don haka zantukansa na da muhimmaci.

Bari mu ƙalailaice lissafi:

Yayin Hajjin 2019, Ƙasar Saudiyya ta ƙara wa Pakistan kujerun Hajji guda 15,000 wanda jimilla ta kama 179,210, wannan ya sanya Pakistan ta zama ƙasa ta biyu daga cikin ƙasashe goma da suka fi yawan maniyyata baya ga ƙasar Indonesiya da ta zo ta ɗaya da adadin maniyyata 221,000.

Idan muka dubi 50,000 da 179,210 za a samu kashi 27.9 idan aka kwatanta da adadin kujerun da Pakistan ta samu a 2019. Lallai abin da ban tsoro.

Idan kuwa haka lamarin yake, to mene ne zai kasance kason 28 na jimillar kujerun Hajjin da Nijeriya ta samu 2019? Amsar wannan tambayar ita ce, maniyyata dubu 26, 600. Kodayake akwai wata dama da Nijeriya ka iya cin moriyarta.

Idan muka dubi Pakistan tana daga cikin ƙasashe 20 da Saudiyya ta haramta wa shiga ƙasar alhali maniyyatan Umura daga Nijeriya na ci gaba da ziyarar ƙasar don aikin Umura.
Sanarwar da Ministan Sha’anin Addini na Pakistan ya yi wanda ba da yawun hukuma ba ne, lamari ne na musamman wanda ba ya rasa nasaba da haramta wa jiragen ƙasa da ƙasa daga Pakistan shiga Saudiyya sakamakon annobar korona.

A ranar 17 ga Mayu Saudiyya ta bada sanarwar buɗe hanya ga jiragen ƙasa da ƙasa don ci gaba da shiga ƙasar, amma duk da haka ta ware waɗancan ƙasashe 20 daga cin moriyar wannan dama. Ƙasashen da Saudiyyar ta haramta wa shigar ta kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Ƙasar ta sanar su ne; Argentina, UAE, Jamus, US, Indonesiya, Ireland, Italy, Pakistan, Brazil, Portugal, UK, Turkiyya, Africa ta Kudu, Sweden, Switzerland, Faransa, Lebanon, Masar, Indiya da kuma Japan.

Mai yiwuwa Nijeriya ta samu riɓi biyu na abin da Pakistan ka iya samu, wato kusan kaso 40 zuwa 50 cikin 100 kenan na kujerun Hajji da muka samu a 2019.

Idan da alamar haske a gare mu dangane da Hajjin 2021 bisa hasashen da ya gabata, wani batun dubawa har wa yau shi ne yadda za a yi rabon kujerun a tsakanin Hukumomin Alhazai na jihohi da kuma kamfanonin Hajji masu zaman kansu.

Zancen da ake yi, tuni wasu jihohi goma da ke kan gaba game da sha’anin Hajji a ƙasar nan kowaccensu har ta yi wa maniyyata sama da 2,500 rajista. Waɗan nan jihohi su ne, Kano, Kaduna, Borno, Katsina, Sokoto, Yobe, Bauchi, Zamfara da kuma jihar Neja. Sai dai, anya ko kamfanoni masu zaman kansu za su samu shiga tsarin rabon kujerun muddin ba a kammala da maniyyatan da jihohi suka yi wa rajista ba.

Ina tunanin hukumar NAHCON na nan na aiki a kan wannan mas’alar, domin kuwa a halin da ake ciki akwai yiwuwar Hukumomin Alhazai na Jihohi sun yi wa maniyyata sama da 40,000 rajista.

Sai dai babban ƙalubalen da ke gaba shi ne, yiwuwar hukumomin alhazai na jihohi su iya tantance adadin maniyyata ta hanyar amfani da tsarin Ma’aikatar Hajji ta lura da shekarun maniyyata daga kundin tattara bayanan maniyyatan da aka yi wa rajista cikin taƙaitaccen lokaci. Wannan dai al’amari ne mai wahalar gaske!

Alal misali, adadin shekarun maniyyata da aka tsayar don Hajjin 2021, tsakanin 20 zuwa 50 ne kamar yadda bayanan Ministan Pakistan suka nuna, sannan ana buƙatar ƙasashe su tura maniyyata kashi 40 cikin 100 na adadin alhazansu yayin aikin Hajjin 2019, yayin da kuma sanarwar haka ta zo ƙasa da kwanaki 40 kafin Ranar Arfa.

Wani al’amarin shi ne galibin jihohi sun ɗauko sunayen maniyyatan 2020 sun gwama su da na 2021. Ga shi kuma a bara duba yawan shekaru babu shi a dokokin yi wa maniyyata rajista saɓanin tsarin rajista na bana.

Na fahimci cewa NAHCON ta bai wa Hukumomin Alhazai Umarni kan su riƙa bada bayanai okaci-lokaci kan adadin maniyyatan da suka yi wa rajista. Kari a kan haka, zai kyautu NAHCON ta bai wa hukumomin umarni kan su soma shirya bayanan maniyyata gwargwadon rukunin shekaru, kamar tsakanin shekara 20 zuwa 50, 20 zuwa 55 da kuma shekara 20 zuwa 60.

Akwai buƙatar shirye-shiryen wayar da kan maniyyata su maida hankali wajen faɗakar da maniyyata buƙatar da ke akwai su kiyaye dokokin kula da lafiya. Haka nan, NAHCON da takwarorinta na jihohi su samar da wata takarda kan sha’anin kula da lafiya a Hajjin 2021, ta yadda za a buƙaci maniyyata ko waɗanda suka ɗaukar musu lamuni su sanya hannu.

Kazalika takardar ta kasance ɗauke da sharaɗin za a janye maniyyaci daga aikin Hajjin 2021 muddin aka samu maniyyaci da take dokar kula da lafiya, walau a Nijeriya ko a Kasar Saudiyya. Na bada wannan shawara ne saboda wasu lokuta wasu ‘yan Nijeriya na da wuyan sha’ani wajen bin doka da oda.

Kawo yanzu, kamata ya yi a ce jihohi na matakin shirya riguna da jakunkunan maniyyata. Za a iya amfani da waɗannan abububuwa a baɗi idan ba a samu zarafin aiwatar da Hajjin 2021 ba.
Ya kamata a soma gudanar da shirin tantance maniyyatan da ke da matsalar rashin lafiya. Duk da dai shirin wayar da kan maniyyata na kan gudana a wasu jihohi, ya kamata NAHCON ta tabbatar da cewa batun dokokin lafiya na daga cikin muhimman abubuwan da ake faɗakar da maniyyatan a kai.

A hanzarta ɗaukar mataki a kan batun biyan rabin kuɗi da kuma jinkirin sanya kuɗaɗen alawus na tafiya cikin asusu da wasu jihohi kan yi tun kafin ƙurewar lokaci. A samu wata dangantaka ta yin aiki tare tsakanin NAHCON da jihohi da sauran takwarorinsu a harkar aikin Hajji domin fahimtar da juna yadda abubuwa ke gudana.

Umarnin da NAHCON ta bai wa Hukumomin Alhazai na Jihohi dangane da yi wa maniyyata rigakafin korona ta yi hakan ne a bisa shawarar Hukumar Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), kuma na tabbata shawarar NPHCDA ba ta rasa nasaba da buƙatar Ma’aikatar Hajji da Umura ta Saudiyya kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka yaɗa.

Ba abu ne da ya dace ba ci gaba da zaman jiran sanarwar Hukumar Hajji da Umura ta Saudiyya a hukumance. Maimakon haka, mu soma ƙwarya-ƙwaryar shirye-shirye sannan mu yi aiki da hasashen Ministan Harkokin Addini na Ƙasar Pakistan kamar yadda Hajj Reporters ta ruwaito a baya.

A ƙarshe, idan muka ɗauki matakin kula da wani al’amari a yadda yake, to, haka lamarin zai ci gaba da zama a yadda yake. Idan kuwa muka faɗaɗa ɗaukar mataki wajen daidaita wani al’amari yadda ya kamata, a ƙarshe haka za mu samu abin da ya kamata.

Fatana ne Hajjin 2021 ya kasance tamkar wani fagen gwaji ga ɗaukacinmu da ke masana’antar Hajji da Umura, kuma tare da haɗin kai da goyon bayan juna ina da yaƙinin za mu iya tunkarar duk wani ƙalubalen da ya tunkare mu har mu kai ga samun nasarar a ƙarshen lamari.

Tabbatar Hajjin 2021 ko akasin haka, yana da kyau mu tuna cewa Allah na jarabtar mu ne da abin da za mu iya ɗauka da kuma magance shi. Faɗar Allah Maɗaukaki, “Allah ba Ya ɗora ma wani rai abin da ya fi ƙarfinsa” [Quran 2:286]

“Haƙiƙa, bayan kowane tsanani sauƙi na tafe”, [Quran 94:5-6], wannan ayar na tunatar da mu cewa a rayuwa, duk wani tsanani ko wahala da aka fuskanta, da sannu sauƙi zai zo daga Allah.

Da fatan Allah Maɗaukaki Ya sanya Hajjin 2021 ya zama makwafi da kuma sakina ga al’ummar Musulmi bisa Hajjin 2020 da aka rasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here