Ganduje ya yi addu’ar zaman lafiya yayin aikin Ummara da iyalinsa

0
312

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi addu’ar Allah Ya bai wa jiharsa Kano da ma Nijeriya baki ɗaya dauwamammen zaman lafiya.

Ganduje ya gabatar da wannan addu’a ne a ranar Laraba sa’ilin da yake gudanar da Umura tare da iyalansa a Saudiyya.

Mai taimaka wa gwamnan kan sha’anin kafafen sadarwa na zamani, Abubakar Aminu Ibrahim, ya ce Ganduje ya yi Umurar ne tare da mai ɗakinsa Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, da ɗansa Engr. Umar Abdullahi Ganduje, da ‘yarsa Dr. Amina Abdullahi Umar Ganduje, sai kuma mai taimaka masa kan harkokin cikin gida, Ahmad Abbas Ladan.

Ibrahim ya ce, gwamnan ya yi wa jiharsa da ƙasarsa addu’ar alheri bayan kammala ibadarsa ta Umura a daren da ya gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here