Ƙasar Saudiyya ta bada ƙa’idojin tafiye-tafiye zuwa wasu ƙasashe 38 a faɗin duniya daga Saudiyya, ciki har da Najeriya.
Sadudiyya ta fitar da ƙa’idojin ne biyo bayan sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta ƙasar ta bayar na ɗage doka hana sufurin ƙasa da ƙasa wanda zai soma aiki daga ranar Litinin, 17 ga Mayu.
Ƙa’idojin wanda aka wallafa su a shafin intanet na ma’aikatar, sun nuna kamfanin sufurin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Saudiyya ya ce dole ne fasinja su duba cancantar tafiyarsu ya zuwa ƙasashen da lamarin ya shafa, sannan wajibi ne a tabbatar an mallaki izinin tafiya idan buƙatar hakan ta taso.
Kamfanin ya ce ana iya samun sauyin ƙa’idojin a kowane lokaci ba tare da wata sanarwa ba. Don haka ya ce akwai buƙatar fasinjoji su kasance masu bibiya tare da neman bayanai kan yadda dokokin tafiye-tafiyen daga wurin jami’ai da kuma amintattun kafofi kafin yin tafiya.
Kazalika, Saudiya ta ce dole ne fasinja ya mallaki shaidar duba lafiya ta PCR faga hannun ɗaya daga cibiyoyin kula da lafiya da aka amince da su a Masarautar.
Ƙasashen da ƙa’idojin suka shafa su ne; Amurka, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Masar, Kuwait, Indiya, Indonesiya, Pakistan, Philippines, Malaysia, Morocco, Spain, Iraƙi, Habasha, Maldives, China, Switzerland, sai kuma Faransa.
Sauran su ne; Tarayyar Turai, Italiya, Austria, Bangladesh, Girka, Jordan, Kenya, Turkiyya, Jamus, Bahrain, Lebanon, Netherlands, Qatar, Singapore, Afurka ta Kudu, Sri Lanka, Sudan, Najeriya, Tunisiya, Oman da kuma Mauritius.