DA ƊUMI-ƊUMI: Saudi ta tabbatar da za a yi Hajjin 2021 amma cikin wani yanayi na musamman

0
2

Ma’aikatar harkokin Hajji da Ummara ta ƙasar Saudi Arebiya a ranar Lahadi ta tabbatar da cewa za a yi aikin Hajji a bana amma cikin yanayin kariyar na lafiya na musamman sakamakon annobar korona.

Ma’aikatar, a wata sanarwar da ta fitar ta ƙara da cewa za a yi Hajjin na bana bayan da a ka yi tanadi na musamman a kan da tsaro domin kariyar mahajjata.

“Hukumar lafiya ta Saudiya za ta ci gaba da yin nazari a kan yanayin domin ɗaukar ƙwararan matakai don ganin cewa an kare lafiyar al’umma.”

Ma’aikatar ta ce nan gaba kaɗan za ta bayyana irin tsare-tsare da tanade-tanaden da ta yi domin tabbatar da an yi aikin Hajjin na bana lafiya ƙalau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here