Muna jiran mu ji tabbacin yin Hajjin bana daga bakin Saudiyya- NAHCON

0
338
ZIKRULLAH NAHCON CHAIRMAN

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta bayyana jin daɗin ta game da bayanin da ya fito daga ƙasar Saudi Arebiya cewa za a yi aikin Hajjin bana, inda ta ƙara da cewa bayanin wani albishir ne gare ta da al’ummar Musulmin duniya baki ɗaya.

A wata sanrwa mai ɗauke da sa hannun Babbar Jami’ar Hulɗa da Jama’a, Hajiya Fatima Sanda Usara, NAHCON ta bayyana cewa, duk da dai Saudiya bata ambata cewa ko ƙasashen duniya za su yi aikin Hajjin na bana ba a taƙaitacciyar sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, hukumar na fatan cewa Hadimin Masallatan Harami Guda Biyu zai bada damar cewa kasashen duniya su je aikin Hajjin na 2021.

Usara ta ce a yayin da hukumar ke tsimayen ƙarin bayani a kan tsare-tsaren da za a yi na Hajjin bana daga Ma’aikatar Harkokin Hajji da Ummara ta Saudiya, NAHCON na kira ga maniyyatan Nijeriya da su ci gaba da haƙuri su kuma ƙara dagewa da addu’a domin a ji bayani mai karfafa gwiwa.

Ta ce “In dai akwai tsarin da zai bawa ƴan kasashen waje su je aikin Hajjin na bana, to NAHCON na da yaƙinin cewa maniyyatan Nijeriya za su samu kujeru ko da kuwa da sharuɗɗa ne. Hakan zai faru ne saboda a halin da ake ciki, ƴan Nijeriya na cikin ƙasashen da aka bawa damar zuwa Ummara kuma Nijeriya ba ta cikin ƙasashen da aka hana zuwa Saudi Arebiya.

“Sabo da haka, shugabancin NAHCON na tabbatarwa ƴan ƙasa, musamman ma waɗan da aka yiwa rijistar zuwa Hajjin bana cewa za ta yi biyayya ga duk wani tsari, sharaɗi da shiri da Ma’aikatar Harkokin Hajji da Ummara ta Saudiya ta gindaya.

“Saboda haka NAHCON na kira ga masu ruwa da tsaki da maniyyata da suma su ɗaura aniyar yin biyayya da tsare-tsaren domin sauƙaƙawa Nijeriya da Saudiya wajen cimma nasarar shirin Hajjin na bana duk da mawuyacin halin da ake ciki

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here