Hajjin 2021: An ƙara samun ƙwarin gwiwa yayin da aka buɗe filin jirgin sama na Madina domin jiragen ƙasashen waje

0
4

A halin da ake ciki, babban filin jirgin sama na Yarima Mohammed Bin Abdulaziz da ke birnin Madinah a Kasar Saudiyya, ya kammala shirye-shiryensa daidai da sharuɗɗan kula da lafiya da ingancin aiki kamar yadda Babbar Ma’aikatar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasar (GACA) ta shata domin bai wa ‘yan ƙasar damar zirga-zirga zuwa ƙasashen ƙetare farawa daga ranar Litinin ta wannan makon.

Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na
Taibah ya yi aiki a ƙarƙashin kulawar GACA domin samar da ƙofar shiga da fita ga matafiya.

Bugu da ƙari, kamfanin ya samar da wata tawaga wadda za ta riƙa bi tana sanya ido kan tabbatar da cewa ana kiyaye dokokin da aka shimfiɗa sau da ƙafa, tare da hana waɗanda matafiya ba shiga wasu muhimman wurare, tabbatar da matafiya sun yi amfani da abin rufe baki da hanci da kuma sanya sinadaran tsaftace hannuwa a ƙofofin shiga da fita fililin jirgin.

Kazalika, hukumar filin jirgin ta samar da wurin tantance matafiya gabanin shiga jirgi domin tantance matsayin lafiyar matafiya da ma’aikata ta hanyar amfani da manhajar ‘Tawakkalna’. Da wannan, ana sa ran babu wani fasinja ko ma’aikaci da zai samu zarfin shiga wuri na ƙarshe wanda daga nan sai shiga jirgi ba tare da an tantance lafiyarsa ba.

Haka nan, hukumar ta sanya na’urorin ɗaukar hoto da sauran abubuwan da suka dace a wurare daban-danan domin tabbatar da tsaron matafiya kafin su bar filin jirgin. Tana mai cewa, duk wanda bai kiyaye dokokin da aka shimfiɗa ba ba, ba shi ba shiga filin jirgin saman.

A cewar hukumar, game da abin da ya shafi fasinjoji kuwa, ana lura da yanayin zafin jikinsu tare da lura da sauran abubuwan da ake buƙatar a sani sannan a miƙa su ga cibiyar kula da lafiya na filin jirgin.

Tuni dai jiragen ƙasa da ƙasa suka soma zirga-zirga a birnin a ranar Litinin inda jirgi na farko ya miƙa daga babban filin jirgin sama na Sarki Khalid da ke Riyadh zuwa babban filin jirgin saman Sarajevo sakamakon ɗage dokar hana zirga-zirga jirage da aka yi a wasu filayen tashi da saukan jiragen sama a Masarautar Saudiyya.

A ranar Litinin GACA ta fitar da bayanan tsate-tsaren da aka shirya don amfanin matafiya ciki har da amfani da sabuwar manhajar nan ta ‘Tawakkalna’ wajen shiga filayen jiragen sama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here