Alhazai daga ƙasashen wajen Saudi Arebiya za su je aikin Hajjin 2021, amma a ƙarƙashin tsananin matakai na kamuwa da kuma kariya daga kamuwa da annobar COVID-19, wato korona, kamar yadda wata kafar yaɗa labarai ta Saudiya Al-Watan ce ta rawaito hakan ranar Alhamis.
A tuna cewa a bara, Saudiya bata bada damar ƙasashen waje su je aikin Hajji sakamakon annobar Korona da ta mamaye duniya.
Wannan matakin na bana kuma ya biyo bayan matsayar da Ma’aikatar Harkokin Hajji da Ummara ta fitar a ranar 9 ga watan Mayu, inda aka gindaya sharuɗɗa masu tsauri kan kariya da kula da lafiya da kuma kula da lafiyar mahajjata.
A farkon watan nan ne ma’aikatar ta ce Hukumomin Lafiya na Saudi Arebiya za su ci gaba da lura da yanayin sannan ta ɗauki duk matakan da suka dace domin kare lafiyar duka alhazai.