Hajjin 2021: Za a fara yiwa maniyyatan Abuja rigakafin korona karo na biyu

0
217

Hukumar Birnin Tarayya (FCTA) ta bayyana cewa za a soma yi wa maniyyatan Abuja allurar rigakafin cutar korona kashi na biyu ya zuwa Litinin, 31 ga Mayu, 2021.

Mai magana da yawun hukumar, Muhammad Lawal, ya ce Daraktan Hukumar Kula da Sha’anin Maniyyata na birnin, Malam Muhammad Nasiru DanMalam, shi ne ya bada tabbacin hakan tare da cewa hukumar Abuja na yin dukkan mai yiwuwa domin ganin maniyyatan yankin sun cika duka sharuɗɗan Hajjin bana.

Daraktan ya ce domin cim ma wannan ƙudiri, Sakatariyar Lafiya ta Abuja ta tanadi wadataccen rigakafin korona wanda za a yi wa maniyyatan daidai da tsarin da Ƙasar Saudiyya ta samar don sauke farali a bana.

Ya ce shirin yin rigakafin zai gudana ne a hedikwatar hukumar inda za a yi wa maniyyatan da suka yi rajista a hedikwatar rigakafin a ranakun Litinin da Talata masu zuwa daga kan ƙarfe tara na hantsi.

Kazalika, ya ce ana sa ran maniyyata daga yankin Abuja Municipal su yi rigakafinsu na farko a ranar Laraba, 2/06/2021yayin da maniyyatan yankin Bwari za su yi nasu rigakafin ran Alhamis, 3/06/2021.

Bugu da ƙari, ya ce ana ana sa ran maniyyatan Gwagwalada su yi tasu allurar ranar Juma’a 4/06/2021, sannan maniyyatan yankin Kuje su bi bayansu a Litinin 7/06/2021.

A cewar DanMallam, a ranar Talata, 8/06/2021 maniyyatan yankin
Kwali za su yi rigakafinsu, yayin da na yankin Abaji za su yi nasu kashi na biyu ran Laraba, 9/06/2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here