Hajjin 2021: An fara yiwa maniyyata rigakafin korona karo na biyu a Jihar Nassarawa

0
187

A halin da ake ciki, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen Hajjin 2021, Hukumar Kula da Walwalar Maniyyata ta Jihar Nasarsawa ta soma yi wa maniyyatan hajjin bana allurar rigakafin korona na AstraZeneca kashi na biyu a sassan jihar.

Yayin da yake rangadin duba yadda shirin bayar da rigakafin ke gudana a tsakanin ƙananan hukuma13 da jihar ke da su, Sakataren Hukumar, Malam Idris Almakura, ya ce yin rigakafin na ɗaya daga cikin sharuɗɗan da dole maniyyatan bana su cika su kafin samu zarafin tafiya hajji.

Almakura ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga maniyyatan kan cewa su yi fatali da raɗe-raɗin da ake ta yaɗawa game da batun adadin kujerun hajjin da za a samu, yana mai cewa har yanzu babu wani bayani da suka samu a hukumance dangane da hakan daga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON).

Daga nan, sakataren ya yaba wa Gwamnan Jihar, Abdullahi Sule da Hukumar Bunƙasa Lafiya bisa irin gudunmawar da suka bai wa hukumar yayin rigakafin farko da kuma na biyu.

Ya kuma gargaɗi maniyyatan kan cewa kowa ya tabbatar da ya samu yin allurar a tsakanin ‘yan kwanakin da aka ware domin yin rigakafin. Tare da cewa duk maniyyacin da ya rasa wannan dama, ya zargi kansa da duk abin da ya biyo baya.

Maniyyatan da suka samu yin nasu rigakafin, sun yi yabo da jinjina ga Sakatare Almakura, wanda ya shige gaba wajen tabbatar da shirye-shiryensu na gudana yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here